Hukumar kula da gandun daji da wuraren shakatawa na birnin Beijing, ta bayyana Talatar nan cewa, an gudanar da bukukuwan al’adu guda 109 a fadin birnin Beijing, albarkacin hutun bikin Bazara na kwanaki 8 da ake gudanarwa.
Ayyukan fasaha sun kara tabbatar da zama wani abin da ke sanya jin dadi ga jama’a a tsawon lokacin hutun. Sama da wuraren shakatawa 15 a babban birnin kasar Sin, ciki har da gidan ibadar aljannar duniya da wurin shakatawa na Beihai, sun tarbi maziyarta da ayyukan fasaha irinsu zane-zane, yin fitilu, da hada alawar sukarin gargajiya, kamar yadda Ma Hong, shugaban ofishin kula da wuraren shakatawa na hukumar ya bayana.
Alkaluman hukuma sun nuna cewa, a matsayin birnin dake janyo masu sha’awar yawon bude ido mafi girma a lokacin bikin Bazara, yawan ziyarce-ziyarcen da mutane suka yi a wuraren shakatawa na birnin Beijing Talatar nan ya zarce miliyan 1.52, dake zama rana ta hudu ta sabuwar shekara, wanda ya karu da kashi 119.45 bisa dari kan na bara. (Ibrahim)