Kasidar mai suna Matsalar Wutar Lantarki: Yadda Wayoyin NEPA Suka Harhade ta nuna yadda a rana daya, aka wayi gari an wargaza kadarorin kasa ta NEPA, aka yi mata wasoso aka kuma kwashe dokiyar kasa da sunan inganta samar da wutar lantarki da kuma wadata ta ga ‘yan Nijeriya.
A ci gaba, wannan bangare zai yi hasashe ne a kan makudan kudade da suka shiga harkar wutar lantarkin Nijeriya daga wasu hanyoyin da suka shafi hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashe da kuma wasu ma’aikatu da suke ba wa gwamnati taimako ko bashi, da kuma dimbin wutar lantarki da aka ce ana samar wa amma ‘yan Nijeriya wanda ba su gani ba a kwaryarsu, da sauran batutuwa masu tayar da hankali da suka taso daga gazawa, rashin fahimta, da rashin gaskiya ,da rashin bin diddigi ,da kuma rashin sanin makamar aiki, daga wadanda aka dauka aiki don tabbatar da cewa an samu wadatacciyar wutar lantarki a Nijeriya. Bayan haka, zai nuna hakokin ma’iakata, da suka ce an rike ba a kuma biya ko basu ba har yan zu, lokacin da aka yi wasoso akan dukiyar kasa ta NEPA /PHCN.
- Mahara Sun Lalata Layin Samar Da Wutar Lantarki Na Gwagwalada-Katampe – TCN
- Kwararren Hada Bama-bamai Da Wani Mutum Daya Sun Yi Saranda A Borno
Dimbin duhu a cikin hasken rana
Bari mu yi la’akari da wasu kididdiga:
Kamfanin sadarwa da raba wuta a Nijeriya (TCN) ta samu lamunin Dalar Amurka miliyan 300 (kimanin Naira biliyan 108.6) daga bankin duniya a shekarar 2010 domin aiwatar da aikin inganta wutar lantarki da iskar gas a Nijeriya (NEGIP).
A Afrilun 2018, Hukumar Hadin Kan Kasa da Kasa ta Japan (JICA) ta ba da tallafin Yen na Japan biliyan 1.317 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 12.4 (kimanin Naira biliyna 4.5) don shigar da na’urorin wutar lantarki (power capacitors da switchgears)
TCN a watan Satumbar 2019 ta ce ta samu lamuni na Dalar Amurka biliyan 1.661 (kimanin Naira biliyan 601.3bn) daga hukumomi biyar don saye da sanya ayyuka a karkashin shirinta na ‘Rehabilitation and Edpansion Program’ (TREP).
Bankin Duniya shi ne ya fi bayar da gudunmawar inda ya bayara da Dalar Amurka miliyan 486 don sabon aikin isar da wutar lantarki ta Nijeriya mai taken (NETAP), da kuma Dalar Amurka miliyan 27 na aikin watsawa mai taken (North Core).
Bankin Raya Afirka (AfDB) ya ba da Dalar Amurka miliyan 410 don ayyukan fadada rarraba wutar lantarki, Hukumar Raya Kasashe ta Faransa (AFD) da Tarayyar Turai (EU) sun ba da Dalar Amurka miliyan 330 don aikin wutar lantarki mai taken (Northern Corridor Transmission Project).
A halin da ake ciki Nijeriya na da GENCOs 25, amma babban layukan wutar lantarki ta Nijeriya (National Power Grid) ta durkushe sau 206 daga shekarar 2010 zuwa 2019, kamar yadda Cibiyar Bincike ta Duniya (ICIR) ta ruwaito. Kalubale ne samun alkaluma na shekarun 2005 zuwa 2009 da kuma daga 2020 zuwa yau.
Duk da durkushewar layukan wutar lantarkin da ke faruwa, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), ta bayyana cewa za ta cire Naira biliyan 10.5 daga cikin ribar kudaden da aka amince kuma aka ba da izini na shekara-shekara ga DISCOs guda 11, a matsayin wani bangare na takunkumi kan rashin bin ka’idojin lissafin kudi da za su caja abokan cinikin su da ba su da mitoci.
Rahoton 2019 na Ofishin Kididdiga na Kasa (NBS) – Rahoton Sashen Makamashi da aka samu kuma aka tura (Energy Generated and Sent Out and Consumed and Load Allocation). Ya nuna:
Jimillar makamashin da GENCOs suka samar kuma aka aika, shi ne 33,448,633 MWh, kamar haka:
a. GENCOs masu zaman kansu – 19,692,683 MWh. b. Masu Samar da Wutar Lantarki (IPP) – 7,798,253 MWh. c. Hadakar Wutar Lantarki ta Kasa (National Integrated Power Project (NIPP) – 5,957,697 MWh.
Ba ri muyi lissafi gwari-gwari: Matsakaicin Kirkirar Makamashi na Kullum =Jimlar Kirkirar Makamashi na Shekara-shekara / Yawan Kwanaki a cikin Shekara.
A. Matsakaicin Karfafa Makamashi na Kullum = MWh 33,448,633 kwanaki 365. B. Matsakaicin Karfafa Makamashi na Kullum = MWh /91,642.28 kowace rana.
A halin yanzu matsakaicin Rarraba Wutar Lantarki (MW) dangane da bayanan NERC kamar yadda ta sanar a shekarar 2021 ya kasance MW 4,094.09.
Tambaya a nan,
Na farko – Me ya faru da kiyasin makamashin MWh 87,000 (91,642.28 – 4,094.09) da ake samarwa a rana?
Na biyu – Me ya sa CBN da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi za su ci gaba da fitar da biliyoyin Naira don samar da makamashin da ba ya isa wajen masu bukatarsa?
Na uku – Menene kuma ya faru da makudan kudade na kasafin kudin shekara-shekara (National Budget) da suka shiga harkar wutar lantarki ba tare da samar da ingantacciyar wutar lantarki ga jama’a ba?
Cin Zali da Rana Tsaka
A lokacin da aka ruguza NEPA/PHCN, akwai ma’aikata kusan 15,000 da aka sallame su, sannan aka mayar da al’amuransu zuwa kamfanin kula da al’amura, da basususka da kuma sauran ababen da suka shafi wutar lantarki na Nijeriya, wato (NELMCO) wanda aka kirkira domin gudanar da ayyukan da ya shafe wa’anan ababe na rusasshiyar PHCN.
To wane wainar aka toya a wannan bangaren?
A cewar Bankin Lamuni (IMF), an kiyasta cewa Nijeriya ta na yin asarar kusan Dalar Amurka biliyan 29 a kowace shekara saboda rashin samar da wutar lantarki isasshe. Bugu da kari, an ruwaito ‘yan Nijeriya na kashe kudade Dalar Amurka biliyan 14 kowace shekara akan janareta da mai don shawo kan karancin wutar lantarki.
Ba makawa rufe Kamfanin Mitar Wutar Lantarki na Nijeriya (EMCON) da take Zariya na Jihar Kaduna tare da asarar ayyukan yi da kuma fitar da makudan kudaden waje zuwa kasashen waje don sayen mitoci sabanin sanya hannun jari a cikin gida.
NELMCO ce ke da alhakin rikewa da sarrafa kaddarorin PHCN da Yarjejeniyar Sayen Wutar Lantarki, tare da ikon siyarwa, ko mu’amala da wadannan kaddarorin don biyan basussuka ko wasu batutuwa masu alaka.
An dora wa NELMCO alhakin karba da gudanar da basussukan da suka makale, kuma ita aka daurawa alhakin sauran alamura da ke da alaka da albashi ko alawus na ma’aikatan rusasshiyar Kamfanin Power Holding Company of Nigeria (PHCN). wannan ya hada da:
Rashin biyan kudin Fansho da Garatuti na bangaren gudummawar kamfanin NEPA/PHCN saboda kashi 7.5% kawai da ma’aikatan ke bayarwa ko wane wata su ne a cikin asusunsu na PFA.
Rashin biyan albashi da alawus-alawus da fakitin sallama na yawancin tsofaffin ma’aikatan kamfanin NEPA/PHCN.
Batu mai ban haushi da ya kunshi kaso 10% na hannun jarin kafanin PHCN na ma’aikatan da aka sallama wanda har yanzu ba a basu ba.
Wani batun kuma da aka kasa warware shi, shi ne horon salama (training) na gida da na waje da kuma bita ga ma’aikatan da aka sallama, wanda ya kasance sharadi ne na sallama ko biyan alawus a madadinsa, har yanzu ba a biya su wannan kudade ba.
Rashin biyan asalin alawus da kuma bashin da suke bi na albashin watanni 16 daga 2012. (Daga lokacin ruguza kanfanin PHCN zuwa kammala mika su ga mutanen da wai su ne ’’Core Inbestors’’).
Rashin biyan kudin inshoran ma’aikatan NEPA/PHCN.
Rashin biyan kudin rangwamen wutar lantarki ga ma’aikatan NEPA/PHCN da aka sallama.
Halin da aka jefa wadanda aka sallama a lokacin wasoson NEPA/PHCN ya kara wani rashin adalci ga labarin, yayin da kuma aka bar su a cikin rudani, da kuma hana su hakkokinsu na hakika. Bayan haka, wadannan sallamammun ma’aikatan an bar su cikin wani yanayi na fargaba da rashin sanin makomarsu game da makudan kudadensu da ya haura kimanin Naira bilyyan 25 ko fiye, bisa ga ikirarinsu.
Bari mu nunfasa haka kada mu samu hawan jinni domin kuwa akwai saura.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.