Rundunar ‘yansandan jihar Taraba a ranar Litinin ta tabbatar da mutuwar wasu mutum hudu sakamakon wutar lantarki a yankin Danyavo da ke Jalingo, babban birnin jihar.
Bayanai sun yi nuni da cewa, an kawo wuta mai karfi ne a unguwar, lamarin da ya janyo bugawar taransifoma har ya janyo hakan.
- Kotu Ta Tabbatar Da Kefas A Matsayin Gwamnan Taraba
- Kotun Zaben Gwamnan Taraba: Cikin Matsi INEC Ta Ayyana Sakamako, A Sake Bitar Zaben – NNPP
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Usman, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Jalingo.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin.
Jami’in ya bayyana cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su, sun hada da Remond Ofonbuk, dan shekara 44 a duniya, da matarsa, Mfonbong Remond, Hevean Remong dan shekara 15, da kuma First Remond dan shekara 13.
Usman ya ce, an ajiye gawarwakin mamatan a dakin adana gawarwaki domin gano hakikanin abun da ya janyo tashin gobarar.