Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Juma’a cewa, a shirye kasarsa take ta hada hannu da Canada domin mayar da dangantakarsu kan turba mai aminci da karfi da dorewa nan ba da jimawa ba, domin jama’arsu su amfana.
Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da firaministan Canada Mark Carney, a gefen taron shugabannin APEC na 32, inda ya ce ya kamata kasashen biyu su rike juna da kyakkyawan ra’ayi mai ma’ana da aminci.
Har ila yau shugaba Xi Jinping ya gana da firaministan Thailand Anutin Charnvirakul, da kuma firaministar Japan Sanae Takaichi, daya bayan daya, a Gyeongju, kasar Koriya ta Kudu yau Jumma’a.
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)














