Al’ummar Sinawa tana da al’adar shuka itace yayin bikin gargajiyar kasar Sin na share kaburbura wato Qingming, don haka ne ma, shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping ya je lambun shan iska dake tsakiyar Dongba a yankin Chaoyang na birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin a jiya Talata 4 ga wata wato gabannin bikin Qingming, domin shuka itatuwa tare da mazauna birnin.
A filin shuka itatuwan, shugaba Xi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu da kuma ‘yan shekaru masu zuwa, samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ita ce babbar manufar raya kasar Sin, kuma idan ana son tabbatar da wannan manufa, ya dace a dogara kan karfin miliyoyin al’ummar kasar baki daya.
Xi ya kara da cewa, shuka itatuwa babban aiki ne mai ma’ana matuka, wanda zai amfanawa al’ummar kasar daga zuriya zuwa zuriya, don haka kamata ya yi a rika gudanar da aikin cikin dogon lokaci. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp