Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan sun shirya liyafa a birnin Harbin na lardin Heilongjiang, domin maraba da zuwan muhimman bakin da za su halarci bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9.
Wadannan muhimman baki sun hada da Sultan na kasar Brunei Haji Hassanal Bolkiah Mu’izzaddin Waddaulah, da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Japarov, da shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, da firaministar kasar Thailand Paetongtarn Shinawatra, da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Koriya ta Kudu Woo Won-shik da dai sauransu.
A yayin liyafar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a wannan karon, gasar za ta samu halartar adadin kasashe da yankuna da ’yan wasannin motsa jiki da ba a taba samun irinsa a cikin tarihinta. Kuma, yana imanin cewa, gasar da za a yi a birnin Harbin za ta nuna kyakkawan hali na musamman na kasar Sin, da kyawun nahiyar Asiya, kana, tabbas ne, za a cimma nasarar gudanar da gasar bisa hadin gwiwar da ke tsakanin hukumar Olympics ta nahiyar Asiya da wakilai na kasashe da yankunan duniya.
Bugu da kari, Xi ya jaddada cewa, babban taken gasar ta wanann karo shi ne “Fatanmu a wannan lokacin na hunturu, da kaunarmu ga nahiyar Asiya”, ya nuna fatan al’ummomin nahiyar Asiya na shimfida zaman lafiya, da neman ci gaba, da sada zumunta a tsakanin bangarori daban daban. (Mai Fassara: Maryam Yang)