Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sun jaddada cewa, ya dace a warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar tattaunawa.
Bangaren Rasha dai ya sake jaddada aniyarsa, ta sake gaggauta dawo da tattaunawar zaman lafiya wanda kasar Sin ta yaba da shi matuka.
Bangaren Rasha yana kuma maraba da aniyar kasar Sin, ta taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin kasar ta Ukraine ta hanyar siyasa da diflomasiyya, kana tana maraba da shawarwari masu ma’ana da aka gindaya, a matsayin kasar Sin kan daidaita rikicin Ukraine a siyasance.
Bangarorin biyu sun yi nuni da cewa, idan har ana son warware rikicin kasar Ukraine, wajibi ne a mutunta halaltacciyar damuwar matsalar tsaron da kasashen duniya suke da ita, da magance yin fito-na-fito na wata kungiya, tare da kaucewa rura wutar rikici.
Haka kuma bangarorin biyu sun jaddada cewa, tattaunawa mai ma’ana, ita ce hanya mafi dacewa ta kawo karshen matsaloli. Don haka, ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga kokarin da ake yi. (Mai fassarawa: Ibrahim)