Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Zambia Hakainde Hichilema sun yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a yau Talata.
Da yake tsokaci kan yadda yake dora muhimmanci kan bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Zambia, Xi ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da shugaba Hichilema, wajen daukar bikin a matsayin wata dama ta sada zumuncin gargajiya, da tabbatar goyon bayan juna, da karfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni, tare da ciyar da harkokin zamanantar da kasa gaba bisa sabon tafarki a sabon zamani, da karfafa hadin gwiwar Sin da Zambia bisa manyan tsare-tsare, da gina al’ummar Sin da Zambia mai kyakkyawar makomar bai daya.
A cikin sakonsa, Hichilema ya ce bikin cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya, wani muhimmin ci gaba ne a dangantakar dake tsakanin Zambia da Sin, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wacce ta ginu bisa mutunta juna, da hadin gwiwar samun nasara tare, da samun wadata tare, ta ba babbar gudummawa ga ci gaban kasashen biyu.
Yana mai cewa, ayyukan hadin gwiwa irin su layin dogo na Tanzaniya da Zambia da tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa mai suna Kafue Gorge Lower Hydropower Station, sun samu sakamako mai kyau, Hichilema ya kara da cewa kasarsa za ta ci gaba da ba da goyon baya ga manyan tsare-tsare kamar su shawarar “Ziri daya da hanya daya” da hadin gwiwa da kasar Sin wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama. (Yahaya)