A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing.
Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar Sarki Sihamoni bikin da za a yi na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin kasar Japan, da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)