Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, daukar matsayar kashin kai da danniya ba za su taba samun goyon bayan al’umma ba. Kuma tarihi ya tabbatar da nacewar sassa duniya ga manufar tasirin sassa daban daban, da dunkulewar tattalin arzikin duniya, da cudanyar mabambantan al’adu, don haka ba wata kasa dake fatan zama saniyar ware.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, lokacin da yake ganawa da shugaban jam’iyyar al’ummar Cambodia, kuma shugaban majalissar dattawan kasar Samdech Techo Hun Sen.
- Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
- Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Ya ce yakin cinikayya na illata tsarin cudanyar mabambantan sassa, da gurgunta tsarin wanzuwar tattalin arziki, don haka kamata ya yi kasashen duniya su dinke waje guda, tare da kankame manufofin tsaron kasashen da ci gabansu. Kazalika, su rungumi tafiya tare bisa martaba juna, da hadin gwiwar bunkasa juna, da neman ci gaban bai daya. Su kuma yi aiki tare wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama.
Shugaban na Sin ya ce a gabar da nahiyar Asiya ke kan turbar sabuwar tafiyar fadodo da kai tare, Sin za ta ci gaba da nacewa ka’idar kawance, da gaskiya, da cimma moriya tare da rungumar kowa da kowa, da manufar bunkasa abota da yin hadin gwiwa tare da kasashe makwaftanta.
Har ila yau, za ta ci gaba da dorawa inda aka tsaya, da tabbatar da daidaito a diflomasiyyar makwaftaka, da zurfafa hadin gwiwar abota da kasashe makwaftanta, ta yadda za su iya kaiwa ga raba fa’idar zamanantarwa irin ta Sin ga dukkanin sassan shiyyar. Bugu da kari, Sin za ta ingiza gina al’umma mai makomar bai daya da kasashe makwaftanta, tare da yin aiki tukuru da sauran sassa don ingiza zamanantar da nahiyar Asiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp