Da maraicen jiya Talata 11 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci birnin Maoming na lardin Guangdong dake kudancin kasar, inda ya yi tattaki zuwa kauyen Baiqiao na garin Genzi dake birnin Gaozhou.
A wajen, shugaba Xi ya yi ziyarar gani-da-ido a lambun shuka wani nau’in kayan marmari mai suna lychee, da ofishin kungiyar hadin-kan manoma, don kara sanin yadda ake gudanar da ayyukan noman lychee, da farfado da yankunan karkarar wajen.
Xi ya yaba da kokarin da manoman wurin suka yi, na samar da ci gaba ga yankunan karkara, ta hanyar raya wasu sana’o’i na musamman, ciki har da noman lychee. Yana mai cewa, ana kiran wurin da sunan “Garin Lychee”, inda sana’ar noman lychee din ta zama wani muhimmin matakin da aka dauka, wajen samar da ci gaba, tare da farfado da yankunan karkara. A cewar sa, akwai makoma mai haske a fannin raya sana’o’i na musamman a yankunan karkarar kasar Sin.
Sannan, shugaba Xi Jinping ya kaiwa sojojin ruwa na rundunar kudanci ta sojojin ’yantar da al’ummar kasar Sin ta PLA ziyara a jiya Talata.
Yayin ziyarar, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin gudanar da horo, da shirin ko-ta-kwana, tare da gaggauta sauye-sauye domin bunkasa zamanantar da rundunonin sojin kasar a dukkanin fannoni. (Murtala Zhang, Saminu Alhassan)