Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada yayin da yake saurari rahoton aikin gwamnati da kwamitin jam’iyyar na lardin Hainan cewa, ya kamata a aiwatar da ayyukan da kwamitin tsakiya na JKS ya tsara kan raya mashigin tekun Hainan na ciniki cikin ‘yanci, da raya yankin gwajin aikin bude kofa da yin kwaskwarima a dukkan fannoni, da yankin gwajin raya sha’anin halittu na kasar, da cibiyar yin sayayya da yawon shakatawa ta kasa da kasa, da kuma yankin samar da hidimomi bisa manyan tsare-tsare na kasar. Kana a yi kokarin raya mashigin tekun Hainan na ciniki cikin ‘yanci a matsayin muhimmin wurin bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin a sabon zamani, da kuma a raya tsibirin Hainan bisa zamanintarwa irin na kasar Sin.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata a sa kaimi ga yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha da kuma sana’o’i, da bunkasa manyan sha’anin yawon shakatawa, da samar da hidimomi, da kimiyya da fasaha, da aikin noma a wurin zafi na musamman da sauransu. Kana a mai da hankali ga fannonin yin ciniki, da zuba jari, da hada-hadar kudi a tsakanin kasa da kasa, da zirga-zirgar jama’a, da yin jigila cikin ‘yanci, da kuma tabbatar da tsaron sadarwa. Hakazalika kuma, a yi kokarin raya tsarin bude kofa ga kasashen waje bisa ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na duniya, don samar da yanayin yin ciniki bisa ka’idojin kasuwanci da dokoki da kuma na duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp