A watan Janairun shekarar 1969, Xi Jinping wanda ke kasa da shekaru 16 ya bar gida, ya tafi aiki a Liangjiehe dake arewacin Shaanxi. Mahaifiyarsa ta dinka masa wata jakar adana kayayyakin dinkin hannu, inda ta dinka wasu kalmomin Sinanci uku masu launikan ja a kan jakar, wadanda ke nufin, fatan mahaifiya.
Xi Jinping ya ce, tun daga haihuwarsa, iyayensa sun kasance tare da shi har tsawon shekaru 48, inda yake matukar fahimta da kaunarsu. A shekarar 2001, Xi Jinping ya rubuta musu wata wasika dake cewa, a ganinsa, iyali shi ne makaranta ta farko a rayuwarsa, kuma su iyayensa, su ne malamansa na farko.
Mahaifiyarsa Qi Xin na fatan danta zai mai da hankali matuka kan aikinsa, domin sauke nauyin dake wuyansa yadda ya kamata. Xi Jinping bai taba mantawa da fatan mahaifiyarsa ba ko kadan. Ya ce, bukatun jama’a su ne a gaban komai, kuma ya kamata ya kaunaci jama’a kamar yadda yake kaunar iyalansa, ta yadda zai kawowa jama’a moriya da kyautata zaman rayuwasu.
Xi Jinping ya sanya muradun jama’a a gaban kome, ya kuma yi iyakacin kokarin kyautata zaman rayuwar jama’ar kasar Sin, matakin da ya cika fatan mahaifiyarsa kwarai. (Amina Xu)