Da yammacin yau Alhamis 8 ga wata, yayin gabatowar sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar kasar Sin, shugaban kasar, Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, sun zanta ta wayar tarho.
Shugabannin biyu sun mika wa juna gaisuwar barka da shiga sabuwar shekara, inda Xi ya jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su karfafa mu’amala da hadin-gwiwa, da kiyaye cikakkun yankunan kasa, da tsaro, da muradun ci gaba, tare da nuna adawa da shisshigin da sauran kasashe suke yi cikin harkokinsu na gida. Ya ce kasar Sin na mara wa Rasha baya, wajen gudanar da harkokinta na jagorantar kungiyar BRICS a shekara ta 2024, da fatan karfafa hadin-gwiwa da mu’amala tare da Rasha, don aiwatar da ra’ayin kasantuwar hulda tsakanin bangarori daban-daban a duniya, da gina duniya mai zaman adalci da daidaito, da dunkule tattalin arzikin duniya bai daya dake amfanawa kowa da kowa.
Shi ma shugaba Putin cewa ya yi, a bana ake cika shekaru 75 da kulla huldar jakadanci tsakanin Rasha da Sin, kuma sakamakon kokarin da kasashen biyu suka yi, dangantakarsu ta kai wani sabon matsayin da ba’a taba ganin irinta ba a tarihi. Ya ce Rasha na fatan karfafa hadin-gwiwa da mu’amala tare da Sin a wasu muhimman tsare-tsaren shiyya-shiyya da na kasa da kasa, ciki har da kungiyar hadin-kan Shanghai wato SCO, da nufin goya wa juna baya, da kiyaye huldar bangarori daban-daban a duniya, da kare halastattun hakkokinsu. Ya kara da cewa, Rasha tana kuma tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma a cewarsa, duk wani yunkuri na hana dunkulewar kasar Sin baki daya, ba zai ci nasara ba. (Murtala Zhang)