Xi Jinping ya kan ce, jama’a sun zabe shi a mukamai daban daban, don haka har kullum ya kan mayar da jama’a a gaban kome.
Ya fito ne a cikin al’umma, yana aiki tukuru ne domin muradun al’umma, kana yana dogara da al’umma. Daga karamin kauye da ke kan tudu mai tsayi zuwa kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, daga sakataren reshen jam’iyyar dake wani karamin kauye zuwa babban sakataren jam’iyyar kuma shugaban kasa, har kullum Xi Jinping yana kishin kasarsa, yana kokarin bautawa jama’a.
Yana ta iyakacin kokarin kawo wa jama’a alheri ba tare da kasala ba, wanda shi ne burin da yake kokarin cimmawa ko da yaushe.
Yana kaunar jama’a, yana aiki tukuru domin jama’a, kamar yadda ya kan ce, ba zai ci amanar jama’a ba, zai bautawa jama’a ba tare da nuna son kai ba. (Tasallah Yuan)