Da safiyar yau Laraba 3 ga wata ne aka shirya babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya a filin Tian’anmen dake Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasa Xi Jinping ya ba da jawabi mai muhimmanci.
A yayin jawabinsa, Xi ya bayyana cewa, yau muna gudanar da gagarumin biki a nan, don tunawa da shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da nufin tuna tarihi, da martaba ’yan mazan jiya, da martaba zaman lafiya da gina makoma mai kyau.
Xi ya kuma wakilci kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta Sin, da majalisar wakilan jama’ar kasa, da majalisar gudanarwa, da majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa, da ma kwamitin koli mai kula da aikin soja don nuna girmamawa sosai ga tsoffin sojoji, da abokan aiki, da ‘yan kishin kasa, da jami’an sojoji na kasar da suka taba shiga yakin kin mamayar dakarun kasar Japan, da kuma dukkan Sinawa dake cikin gida da waje, wadanda suka ba da babbar gudunmawarsu ga cimma nasarar yakin kin tafarkin murdiya.
Kana ya yi godiya da zuciya daya ga gwamnatoci, da abokai na kasa da kasa da suka taba nuna goyon baya, da taimakawa Sinawa wajen kin mamayar dakarun kasar Japan, da kuma lale marhabin ga baki daga sassan kasa da kasa da suka zo don halartar bikin.
Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun Japan wani muhimmin bangare ne na yakin duniya na biyu, inda al’ummar kasar Sin suka yi babbar sadaukarwa don ceto wayewar kan dan adam da kuma kare zaman lafiya a duniya.
Tarihi ya yi mana gargadi da cewa, makomar dan adam tana hade da juna, kuma kowace kasa, da kowace kabila dole ne su daidaita da juna, su zauna lafiya, su taimaki juna, domin ta haka ne kawai za a iya kiyaye tsaro na gama gari, da kawar da tushen yaki, da tabbatar da tarihi bai maimaita kansa ba!
A jawabin nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, al’ummar kasar Sin babbar al’umma ce mai dogaro da kanta, wadda ba ta jin tsoron masu nuna karfin tuwo. A lokutan baya, an sha fama da gwagwarmaya tsakanin adalci da mugunta, tsakanin haske da duhu, tsakanin ci gaba da koma baya, kuma jama’ar kasar Sin sun hada kai sun tashi tsaye wajen yaki da abokan gaba don wanzar da rayuwar kasa, da farfado da al’umma, da tabbatar da adalci ga dan Adam.
A yau, dan Adam na fuskantar zabi na zaman lafiya ko yaki, da tattaunawa ko nuna adawa, da samun nasara tare ko kin hadin gwiwa. Jama’ar kasar Sin suna tsayawa tsayin daka kan gaskiya da ci gaban wayewar kan dan Adam, tare da bin hanyar ci gaba cikin lumana, kuma suna aiki tare da jama’ar kasa da kasa don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
Ya ce ya wajaba daukacin dakarun sojojin kasar su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya, su hanzarta gina rundunar sojoji ta zamani, tare da nacewa kare ’yancin kan kasar Sin, da hadin kai da kare kimar yankunan kasar.
Kazalika, shugaba Xi ya yi kira ga daukacin dakarun sojojin kasar da su samar da tsare-tsare na farfadowa da daukacin kasar Sin bisa babban matsayi, tare da bayar da gagarumar gudummawa wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Bilkisu Xin, Amina Xu, Safiyah Ma, Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp