Jiya Laraba 10 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Kongo (Kinshasa) Félix-Antoine Tshisekedi, dangane da bala’in mamakon ruwan sama da ya yi barna a kasar.
Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Kongo (Kinshasa), ta fuskanci ruwan sama mai karfi a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi da dama. Ya ce a madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, yana mika ta’aziyya ga iyalan wadanda bala’in ya shafa, da juyayi ga iyalan wadanda bala’in ya shafa, da wadanda suka jikkata, da jama’ar yankunan da bala’in ya shafa.
Ya kuma yi imanin cewa, Kongo (Kinshasa) za ta iya shawo kan matsalolin da take fuskanta, tare da sake gina kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp