Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa sakon malamai da daliban jami’ar koyar da ilmin watsa labarai ta kasar Sin wato Communication University of China a Turance. A cikin sakon da ya rubutawa malamai da daliban, shugaba Xi ya yi musu fatan alheri a daidai lokacin da ake cika shekaru 70 da kafuwar jami’ar.
Xi ya jadadda cewa, a cikin sabon karni, yana fatan za su sauke nauyin dake wuyansu na tabbatar da koyar da dalibai nagartaccen ilimi, da daukar aikin watsa labarai da muhimmanci. Yana kuma fatan jami’ar za ta yi amfani da fifikonta wajen zurfafa tsarin yin kwaskwarima da kirkire-kirkire da ma daga karfin ba da ilmi da bincike, da kara mai da hankali wajen horar da kwararru dabarun watsa labarai, don kara taka rawa wajen bautawa kasar Sin a fagen yayata nagartattun ra’ayoyi da al’adu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp