A kwanakin baya, shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin soja na kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya amsa wasikar dukkan hafsoshi da sojojin rundunar sojan sama ta laima mai zaman abar koyi, inda ya yaba musu tare da taya su murnar ranar kafuwar rundunar soja ta kasar Sin.
Wannan rundunar sojan sama ta laima ta zama abar koyi tare da samun lambobin yabo da dama. A shekarar 2013, shugaba Xi Jinping ya ba da umurnin yi wa wannan rundunar sojan sama ta laima lakabi da “abar koyi”. A kwanakin baya, dukkan hafsoshi da sojojin rundunar sun rubuta wasika ga shugaba Xi Jinping, don yin bayani game da tunaninsu da ayyukansu a shekarun baya-baya nan, tare da ba da ra’ayinsu da imaninsu na sanin ayyukan dake bisa wuyansu, da aiwatar da ayyukansu, da kuma samun karin nasarori a nan gaba. (Zainab)