A yayin da aka zaba gami da karrama fitattun injiniyoyin kasa karo na farko, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni mai muhimmanci, tare da taya murna ga “Fitattun injiniyoyi na kasa” da ma “Fitattun kungiyoyin injiniyoyi na kasa” da aka karrama.
Xi Jinping ya jaddada cewa, idan muka fuskanci gaba, dole ne mu kara habaka horo mai zaman kansa na injiniyoyi masu basirar fasaha, da ci gaba da inganta matsayin zamantakewar injiniyoyin, da samar musu da yanayi mai kyau don zama masu hazaka da ba da gudummawa, da kuma hanzarta gina wata babbar kungiyar kwararrun injiniyoyi. Yana kuma mai fatan ganin dimbin masu aikin injiniyanci a duk fadin kasar za su tsaya tsayin daka kan manufar yi wa kasar hidima ta hanyar kimiyya da fasaha da kuma amfanar da jama’a, da jajircewa wajen cimma nasara a muhimman fasahohin zamani, da habaka sabon karfin samar da kayayyaki da ya daukaka na zamani, kana da ba da hidima ga ci gaba mai inganci, da kuma ba da gudummawarsu wajen inganta aikin gina kasa mai karfi da farfado da al’umma a dukkan fannoni ta hanyar zamanantar da kasar Sin.
Mutane 81 ne suka lashe lambar yabo ta “Fitattun injiniyoyi na kasa”, yayin da kuma kungiyoyi 50 ne suka lashe taken “Fitattun kungiyoyin injiniyoyi na kasa”. (Mai fassara: Bilkisu Xin)