Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni kan ayyukan kiyaye abubuwan al’adu da aka gada daga kaka da kakani da ba na kaya ba, inda ya jaddada cewa, shigar da fasahar samar da shayi bisa al’adar gargajiyar kasar Sin cikin jerin sunayen abubuwan al’adu da aka gada daga kaka da kakani da ba na kaya ba, wanda hukumar kula da ilmi da kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO ta gabatar, yana da ma’ana sosai wajen yayata al’adun gargajiyar kasar Sin ta fuskar shayi.
Xi ya kara da cewa, wajibi ne a kiyaye abubuwan al’adu da aka gada daga kaka da kakani da ba na kaya ba bisa tsari, a kokarin biyan karuwar bukatun jama’ar kasar ta fuskar al’adu da tunani da kuma kara azama kan amincewa da al’adun kasar Sin. Haka kuma, wajibi ne a rika kyautata da bunkasa nagartattun al’adun gargajiyar kasar Sin ta hanyar yin kirkire-kirkire, a kokarin inganta hadin kan al’ummar Sinawa da tasirin al’adunsu, da zurfafa yin mu’amala da koyi da juna tsakanin mabambantan al’adu, da watsa bayanan da suka shafi nagartattun al’adun gargajiyar kasar Sin ta hanyar da ta dace, da yayata al’adun Sinawa a ketare. (Tasallah Yuan)