Yau ranar 29 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da masharwacin shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a matsayin manyan kasashen duniya, ya kamata Sin da Amurka su dauki nauyin dawainiyar harkokin jama’a da duniya da tarihi, da kuma sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da samun bunkasuwa tare a duniya.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
- YANZU-YANZU: Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago Ajaero Ya Tafi Amsa Gayyatar Ƴansanda
Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye kokarin raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka mai dorewa yadda ya kamata. Kuma Sin tana fatan Amurka ta nuna ra’ayi mai dacewa kan harkokin Sin da bunkasuwar kasar Sin, da yin kokari tare da kasar Sin don neman hanyar raya dangantakarsu yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, mataimakin shugaban sojoji na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin Zhang Youxia ya gana da Sullivan a wannan rana, inda ya bayyana cewa, batun yankin Taiwan batu ne mai muhimmanci dake shafar moriyar kasar Sin, kana batu ne mafi muhimmanci dake shafar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Zainab Zhang)