Da yammacin yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavro, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, bangaren Sin na goyon bayan al’ummun kasar Rasha su bi hanyar ci gaba da ta dace da yanayin kasarsu, da kuma goyon bayan bangaren Rasha wajen yaki da ayyukan ta’addanci, da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a kasar. Har ila yau, bangaren Sin ya dade da dora muhimmanci kan ci gaban dangantakar Sin da Rasha, yana kuma fatan inganta mu’ammalar bangarorin biyu tare da Rasha, da hada kan kasashe masu tasowa bisa ruhin daidaito, da yin komai a bude, da gaskiya, da kuma hakuri, ta yadda za a inganta kwaskwarimar tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, da jagorantar gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.
- Rikicin Sansanonin ‘Yan Bindiga Ya Ci Rayuwar Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda, Ɗangote Da Yaransa
- Jami’an Tsaro Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga Na Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Abinci A Katsina
A nasa bangare mista Lavro cewa ya yi, dangantakar Rasha da Sin ta bunkasa, a kan tushen daidaito da cimma moriyar juna, ta kuma zarce dangantakar kawance a lokacin yakin cacar baki, wanda hakan ya nuna babbar juriyarta.
Ya ce bangaren Rasha, na fatan yin aiki tare da bangaren Sin, don cimma matsayar da shugabanin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za a ba da gudummawa ga kafa ka’idojin kasa da kasa masu adalci. (Safiyah Ma)