Da yammacin yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing na kasar Sin.
A yayin ganawar, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Amurka su zama abokai, a maimakon abokan gaba, kana su samu bunkasuwa tare, a maimakon kawo matsala ga juna, da neman ra’ayi daya da amincewa da bambance-bambancensu, a maimakon yin mugun takara da juna, da kuma cika alkawarinsu.
- Yanzu-yanzu: Wasu Magina Sun Makale A Baraguzan Wani Gini Da Ya Rushe A Kano
- An Kaddamar Da Bikin Nune-nunen Shirye-shiryen Bidiyo Da Sinima Na Kasar Sin A Kasar Serbia
Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da bangarorin da suke son yin hadin gwiwa da ita. Sin ba ta jin tsoron yin takara, amma ya kamata a yi hakan don samun bunkasuwa tare, a maimakon cin moriya da faduwar wani. Kana kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan kauracewa kafa kawance, kuma tana fatan Amurka ba za ta kafa kawancenta, da nufin yin adawa da Sin ba. Bangarorin biyu suna da abokan huldarsu, amma babu bukatar nuna kiyayya da juna da kawo matsaloli ga juna.
A nasa bangare, Blinken ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar kalubale mai sarkakiya a duniya, ana bukatar Amurka da Sin su yi hadin gwiwa wajen tinkarar kalubalen tare. A yayin ziyararsa a kasar Sin, ya gano bangarori daban daban na Amurka dake kasar Sin suna son kyautata dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin. Amurka ba za ta ta da sabon yakin cacar baka, da canja tsarin kasar Sin, da dakile bunkasuwar kasar Sin, da kin amincewa da Sin ta hanyar kafa kawance, da kuma ta da rikici da kasar Sin ba. Amurka ta tsaya tsayin daka kan manufar “Sin daya tak a duniya”, kana tana son kiyaye yin mu’amala da kasar Sin, da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a birnin Los Angeles, da neman karin hadin gwiwa, da magance rashin fahimtar juna, da daidaita matsalolinsu, ta hakan za a sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin yadda ya kamata.
Yau Jumma’a, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Amurka Antony Blinken a birnin Beijing, a ci gaba da ziyarar aiki da mista Blinken din ke yi a nan kasar Sin.
Yayin zantawarsu, Wang Yi ya yi tsokaci kan huldar kasashen biyu. A cewarsa, huldar kasashen biyu tana dan kara kyautata karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, amma a wani bangare na daban, wasu abubuwan dake kawo cikas ga huldarsu na kara karuwa.
Wang, ya kuma jadadda cewa, Sin na tsayawa kan raya huldar kasashen biyu bisa ra’ayin kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, kuma tana tsayawa tsayin daka kan ka’idar da Xi Jinping ya gabatar, wato mutunta juna, da zama tare cikin lumana, da hadin kai, da cin moriya tare.
Kaza lika, Sin na fatan bangarorin biyu za su mai da hankali kan muradun da suka fi jawo hankalinsu, da fatan Amurka za ta kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da yiwa bunkasuwar Sin matsin lamba. Kana ta kauracewa keta tushen muradun Sin, wato bangaren ikon mulkin kasar, da tsaro da bunkasuwa. (Zainab Zhang&Amina Xu)