A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta kasa da kasa Thomas Bach, wanda ya isa birnin Hangzhou, don halartar bikin bude gasar wasan motsa jiki ta kasashen Asiya karo na 19.
Yayin tattaunawar ta su, Xi Jinping ya nuna cewa, Sin na fatan yin hadin kai da kwamitin, don bude wani sabon babi na hadin kan bangarorin biyu, ta yadda za su taka rawar gani wajen ingiza gasar Olympics, da kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.
A dai yau din, Xi Jinping ya gana da yarima mai jira gadon masarautar Kuwait Mishal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, da mukaddashin shugaban kwamitin shirya gasar Olympic na Asiya ko OCA a takaice, mista Raja Randhir Singh, da takwaransa na Syria Bashar al-Assad wadanda za su halarci bikin bude gasar ta birnin Hangzhou. (Amina Xu)