Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabannin hukumomin tafiyar da harkokin gwamnati da dokoki da shari’a na yankin Macao a yau da yamma. A yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, karkashin jagorancin kantoman yankin Macao Ho Iat Seng, hukumomin gwamnati da dokoki da shari’a na yankin Macao sun aiwatar da manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu a dukkan fannoni, da aiwatar da ayyukansu bisa kundin tsarin mulki da dokokin yankin yadda ya kamata, wadanda suka samar da gudummawa wajen samun wadata da zaman karko a yankin.
Har ila yau, shugaba Xi ya gana da mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Ho Hau Wah da tsohon kantoman yankin Macao Chui Sai On, inda ya bayyana cewa, cikin shekaru 25 da dawowar yankin Macao kasar Sin, an samu babban canji da manyan nasarori a yankin. Ya ce shugabannin biyu, sun taba zama kantoman yankin Macao, inda suka jagoranci gwamnati da bangarori daban daban na yankin wajen tabbatar da tsaron kasa da samun wadata da zaman karko a yankin, ta yadda aka aza tubalin samun bunkasuwa mai dorewa a yankin.
Hakazalika, shugaba Xi ya gana da kantoman yankin Hong Kong Lee Ka Chiu John, wanda ya je Macao don halartar bikin cikar yankin shekaru 25 da dawowa kasar Sin, inda shugaba Xi ya bayyana cewa, manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu ta shiga sabon mataki, kuma ya kamata yankin Hong Kong da yankin Macao su kara kokarin samun sabon ci gaba, kuma su yi koyi da juna da kara mu’amala da hadin gwiwa don samar da kyakkyawar makomarsu. (Zainab Zhang)