Jiya Juma’a, a birnin Moscow na kasar Rasha, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasashe daban daban, wadanda suka hada da shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, da mai jagorantar gwamnatin kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Cuba, kana shugaban kasar Cuba, Miguel Diaz-Canel Bermudez, da shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro Moros, gami da firaministan kasar Slovak, Robert Fico.
Bayan haka, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi, shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, zai ziyarci kasar Sin, tsakanin ranar 10 zuwa 14, ga watan Mayun da muke ciki. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp