Yau Talata 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Mirjana Spoljaric Egger, shugabar kwamitin kasa da kasa na Red Cross wato ICRC a takaice a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.
A yayin ganawar, Xi Jinping ya yaba da nasarorin da ICRC ya cimma kan ayyukan da ya gudanar a fannin jin kai na kasa da kasa tun bayan kafuwarsa shekaru 160 da suka gabata, ya kuma yaba da muhimmiyar gudunmawar da ICRC ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya.
A nata bangaren, Mirjana Spoljaric Egger ta taya kasar Sin murnar zama kasar da ta fi samun yawan lambar yabo ta Nightingale karo na 49, wanda ke nuna yadda ICRC da sauran kasashen duniya suka amince da nasarorin jin kai da kasar Sin ta samu. A ko da yaushe kasar Sin tana mutuntawa gami da aiwatar da dokokin jin kai na kasa da kasa. Aikin raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin kai ya inganta ci gaban duniya tare da ba da gudummawa ga ayyukan jin kai na duniya baki daya. Ta kara da cewa, kwamitinta ya yaba da irin rawar da kasar Sin take takawa, da kuma muhimmiyar gudummawar da take bayarwa ga ayyukan jin kai na kasa da kasa, kuma tana fatan kara zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen ba da sabbin gudummawa tare don sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya gami da ayyukan jin kai na kasa da kasa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)