Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan da suka fito daga sassan masana’antu da cinikayya na kasa da kasa a nan birnin Beijing.
Yayin ganawar, Xi ya jadadda cewa, a cikin shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin musamman ma cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta cimma gaggaruman nasarori wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da dorewar walwalar al’umma dogaro da jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato jKS da kokarin al’ummar Sinawa cikin hadin kai, kuma ba za a raba wadannan nasarori da taimakon da kasashen duniya ke ba ta ba, cikin hadda gudunmawar da kamfanonin ketare dake kasar Sin suke bayarwa.
- Kwarewar Kasar Sin Da Ci Gabanta A Fannin Fasaha Na Da Muhimmanci Wajen Inganta Zamanantar Da Afirka
- ‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
Ban da wannan kuma, Xi ya ce, kasancewarta muhimmiyar kasar dake taka rawar gani da tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya, yanzu kasar Sin tana kokarin zamanantar da kanta a duk fannoni. Ya ce bude kofa wata manufa ce mai tushe da Sin take aiwatarwa, kuma tana kokarin kara inganta wannan tsari a kai a kai, da habaka bude kofa a bangaren ka’idoji da manufofi da ma’auni da sauransu. Ba shakka Sin za ta habaka bude kofarta, da nace wa ga manufar amfani da jarin waje. Hakan ya sa, Sin ta zama wuri mai kyau dake samar da yanayi mai tsaro da inganci ga jarin waje a ko da yaushe.
Shugabanni da manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa fiye da 40 sun halarci taron. Sun kuma nuna cewa, kimiyya da fasaha na taka rawar gani ga sauya salo da daga matsayin masana’antun kasar Sin. Matakin da zai taimaka wajen samun bunkasuwa mafi inganci da dorewa, kuma shi ya sa suke ganin, tattalin arzikin Sin na da makoma mai haske. Kazalika, sun ce Sin ta rika habaka bude kofarta ga ketare duk da cewa ana fama da manufar kariyar cinikayya a duniya, abin da ya baiwa tattalin arzikin duniya tabbaci, har ya sa Sin ta zama tabbataccen wurin da ya fi dacewa da zuba jari. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp