Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya isa birnin Hanoi, fadar mulkin kasar Vietnam ta jirgin sama na musamman a yau Talata bisa agogon wurin, inda ya fara ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta Vietnam Nguyen Phu Trong, da shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam Vo Van Thuong suka yi masa.
Yayin jawabin da Xi ya gabatar a filin jiragen sama na Hanoi, ya bayyana cewa, Vietnam muhimmiyar kasa ce a Asiya, kuma muhimmiyar mamba ce a kungiyar ASEAN. Ya ce a ’yan shekarun baya, bisa jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Vietnam, jama’ar kasar Vietnam suna aiki tukuru don binciken hanyar ci gaba da ta dace da yanayin kasarsu, kuma ana inganta hanyar gyare-gyare a dukkan fannoni, kana tasirin kasar a cikin yankuna, har ma da duniya baki daya na ci gaba da karuwa.
Ya kara da cewa, kasashen Sin da Vietnam suna kusa da juna, an kuma kulla abokantakar gargajiya tsakaninsu tun da can. Kaza lika dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Vietnam da tsoffafin shugabannin kasashen biyu suka kafa wadda ta samu bunkasawa, arziki ne mai daraja na al’ummun kasashen biyu. Har ila yau, bangaren Sin yana daukar bunkasar dangantakar kasashen Sin da Vietnam a matsayin abu mai muhimmanci, yayin da Sin take kokarin raya dangantakar diplomassiya tare da kasashe makwabta.
Xi Jinping ya kara da cewa, yana sa ran a yayin wannan ziyarar aiki, zai yi musayar ra’ayi tare da shugabannin kasar Vietnam, game da wasu abubuwa masu muhimmanci, da jagoranci, da batutuwa masu alaka da kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, wadanda kasashen biyu suke damuwa da su, da kuma jam’iyyun siyasa na kasashen biyu, ta yadda za a kai dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon mataki. (Safiyah Ma)