Da yammacin Alhamis din nan ne, shugaban kasar Sin kana sakantaren hukumar kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar jam’iyyar JKS Xi Jinping ya jagoranci taron kwamiti karo na 2, don nazarin wasu batutuwa ciki hadda kiyaye gonaki da kyautata kasa mai gishiri da kanwa.
A cikin jawabin da Xi Jinping ya bayar, ya jadadda muhimmancin samar da hantsi, kuma gonaki su ne tushen samar da hatsi, don haka dole ne a kiyaye su, da kara ingancinsu, ta yadda za a fitar da boyayen karfin kasa mai gishiri da kanwa, da ma kara karfin samar da amfanin gonaki a duk fannoni. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp