Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin gwiwar mayar da hankali kan ci gaba mai inganci da inganta karfinsu na samar da hidimomin jin kai.
Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kwamitin koli ta sojin kasar, ya bayyana haka ne cikin wasikar da ya rubuta ga kungiyar a yayin da take bude babban taronta karo na 12, yau Laraba a birnin Beijing. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp