Kwanan baya, shugaba Xi Jinping ya mayar da martani ga wasikun da abokai daga bangarori daban daban na kasar Brazil suka aike masa, inda ya karfafa musu gwiwa game da ci gaba da ba da gudummawarsu, wajen sada zumunta tsakanin Sin da Brazil.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da kasar Brazil, don ci gaba da inganta dangantakar abokantaka ta zamani, ta yadda dangantakar dake tsakanin Sin da Brazil za ta zama abun koyi na hadin kai, da samun ci gaba tare, da samun moriyar juna, da kuma samun nasara tare tsakanin manyan kasashe masu tasowa, da kuma bayar da gudunmawa wajen inganta sha’anin zaman lafiya da ci gaban bil’ adama.
Kwanan baya, wasu mutane fiye da dari daga Brazil, sun aikewa shugaba Xi Jinping wasiku, inda a cikin su suka bayyana godiya ga gwamnati, da kamfanoni, da jami’o’i na kasar Sin, bisa gudummawar da suka bayar wajen kyautata mu’amalar sada zumunta tsakanin Brazil da Sin, da inganta rayuwar jama’ar Brazil. (Safiyah Ma)