Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi.
Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya raba ta da zamanantar da aikin gona da kauyuka. Don haka dole ne kwamitocin JKS, da gwamnatoci na sassan kasar su aiwatar da shawarwari da tsare-tsare na kwamitin kolin JKS, da tsayawa tsayin daka wajen raya aikin gona da kauyuka, da kyautata manufofi don karfafawa, da amfana, da wadatar da manoma, da karfafa goyon bayan kayayyakin aikin gona na kimiyya da fasaha, da mayar da hankali kan inganta cikakken karfin samar da amfanin gona, da aiwatar da matakai da dama don inganta ayyukan yi, da kara samun kudin shiga na manoma, da kuma sa kaimi ga farfadowar kauyuka a dukkan fannoni. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp