A madadin kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwar kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar ga al’ummar Sinawa yayin wata liyafar da aka yi yau Alhamis a birnin Beijing.
Shugaba Xi ya gabatar da jawabi a yayin liyafar wadda aka yi a dakin taron jama’a na birnin Beijing, inda ya mika gaisuwa ga Sinawa ‘yan kabilu daban daban da ‘yan uwa da ke Hong Kong da Macao da Taiwan da kuma Sinawa mazauna ketare.
- Yadda Nijeriya Ta Taka Rawar Gani Har Zuwa Zagayen Karshe Na Gasar AFCON
- Kusan Kaso 90 Na Wadanda Suka Amsa Wata Kuri’ar Ra’ayin Jama’a A Duniya, Sun Ce Rikici Tsakanin Bangarorin Amurka Na Neman Zama Jiki
Shugaba Xi ya ce, cikin shekarar da ta gabata, kasar Sin ta nacewa akidar neman ci gaba yayin da take tabbatar da zaman karko da inganta farfadowar tattalin arziki.
Da yake lissafo ci gaban da aka samu, shugaba Xi ya ce yawan hatsin da ake samarwa ya kai sabon matsayin koli, kuma an samu manyan nasarori a bangaren kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. Ya ce gyare-gyare da bude kofa sun ci gaba da zurfafa a kasar Sin, kana muhallin halittu ya ci gaba da kyautata, baya ga sabbin matakai da aka dauka na zamanantar da tsarin tsaron kasa da rundunonin sojin kasar.
Xi ya bayyana cewa, a shekarar 2024 za a cika shekaru 75 da kafa Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, kuma shekarar tana da muhimmanci wajen cimma muradu da burikan dake cikin shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 14, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025.
A cewarsa, Sinawa sun yi imanin cewa dabbar Loong, ko Dragon a Turance, alama ce ta karfi da rashin tsoro da kyautatawa. A don haka ya yi fatan a cikin shekarar Dragon dukkan Sinawa za su kara samun ci gaba cikin jajircewa da karsashi, da hada hannu wajen bude wani sabon babin ci gaba a yunkurin zamanantar da kasar.
A bana, ranar 10 ga watan ne za ta kasance ranar ta 1 ta sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)