Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya ziyarci al’ummar Sinawa tare da shiga shirye-shiryensu na murnar Bikin Bazara na sabuwar shekarar Sinawa, yayin rangadin da ya yi a wani yankin masana’antu a lardin Liaoning na arewa maso gabashin kasar Sin daga Laraba zuwa Jumma’a.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan sojin kasar, ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga al’ummar Sinawa, yana musu fatan samun farin ciki da koshin lafiya, tare da yi wa kasar fatan ci gaba da samun zaman lafiya da wadata, a Shekarar Maciji.
A bana, bikin sabuwar shekarar Sinawa ko Bikin Bazara, ya fado ne a ranar 29 ga watan Janairu, biki ne dake zaman mafi muhimmanci a kalandar gargajiya ta Sin, haka kuma lokaci ne da iyalai kan hadu. (Fa’iza Mustapha)