A yau Lahadi 19 ga watan nan ne babban sakataren kwamitin tsakiyan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya Cheng Li-wun murnar zama shugabar jam’iyyar Kuomintang wato KMT ta kasar Sin, inda ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, jam’iyyun kasar Sin guda biyu, wato JKS da KMT, suna ta kokarin sa kaimi ga bunkasa mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan na kasar Sin, bisa tushen daidaito da aka cimma a shekarar 1992, da kin amincewa da raba yankin Taiwan daga kasar Sin.
Kazalika, gabobin biyu sun yi kokarin tabbatar da zaman lafiya da karko a tsakaninsu, da kara sada zumunta a tsakanin jama’arsu baki daya. Kuma kawo yanzu an rika an cimma wasu nasarori. Shugaba Xi ya yi fatan jam’iyyun biyu za su ci gaba da bin tushen siyasa, da hadin kan al’ummun yankin, da zurfafa hadin gwiwarsu, don sa kaimi ga samun ci gaba tare, da dinkewar dukkanin sassan kasar Sin, da tabbatar da dunkulewar al’ummun kasar Sin, da kiyaye moriyar al’ummun gabobin biyu, da samun kyakkyawar makomar al’ummar kasar Sin baki daya.
A dai yau din, sabuwar shugabar jam’iyyar KMT Cheng Li-wun, ta amsa sakon, tana mai godiya ga shugaba Xi Jinping, tare da bayyana cewa, daukacin jama’ar gabobin biyu al’ummar kasar Sin ne, don haka ya kamata jam’iyyun biyu su kara bunkasa mu’amala, da hadin gwiwa a tsakanin gabobin biyu, da sa kaimi ga zaman lafiya da karko a yankinsu, don amfanar jama’ar gabobin biyu, da kirkiro kyakkyawar makomar farfado da al’ummar kasar Sin. (Zainab Zhang)