A yau Laraba shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Patrick Herminie bisa zabensa da aka yi a matsayin shugaban Janhuriyar Seychelles.
Da yake bayyana kasashen biyu a matsayin dadaddun abokai, shugaba Xi ya ce bangarorin biyu sun mara wa juna baya kan batutuwan da suka shafi muradunsu da sauran manyan batutuwa, kuma hadin gwiwarsu a bangarorin da suka shafi ginin ababen more rayuwa da ci gaba bisa raya muhalli sun haifar da kyawawan sakamako.
Ya kara da cewa, a badi za a cika shekaru 50 da kulla hulda tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa yana daukar batun raya dangantakar Sin da Seychelles da muhimmanci.
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)