Yau Lahadi 3 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya Shehbaz Sharif murnar zama firaministan kasar Pakistan.
A sakon nasa, shugaba Xi ya ce, yana da yakinin cewa, a karkashin jagorancin firaministan gami da sabuwar gwamnatin Pakistan, tare kuma da hadin-gwiwa da kokarin bangarori daban-daban na kasar, babu shakka Pakistan za ta iya samun karin nasarori a sha’anin samar da ci gaban kasa.
Firaministan kasar Sin Li Qiang shi ma ya taya Shehbaz Sharif murna. (Murtala Zhang)