Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasika daga daukacin malamai da daliban jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin, inda ya taya dukkan malamai da dalibai da ma’aikatan jami’ar, da kuma wadanda suka kammala karatu a jami’ar murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar.
Xi ya yi fatan jami’ar za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, da kudurce aniyar inganta aikin gona don amfanin kasa, da kuma zurfafa yin gyare-gyare kan hanyoyin koyarwa da ilmantarwa, da kara kokarin bincike, da kirkire-kirkire a fannin aikin gona, da kuma amfani da sakamakon binciken yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga horar da karin kwararrun masana a fannin aikin gona, don ba da sabuwar gudummawa ga karfafa karfin kasar Sin ta fannin aikin gona, da sa kaimi ga zamanantar da kasa bisa salon kasar Sin. (Amina Xu)














