Da yammacin jiya Talata zuwa safiyar yau Laraba, shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya ziyarci birnin Baoji na lardin Shaanxi da birnin Tianshui na lardin Gansu domin bincike da rangadi.
A birnin Baoji, Xi Jinping ya yi rangadi a gidan adana kayan tagulla na birnin da kuma lambun shan iska na Weihe, domin fahimtar yanayin da ake ciki a wurin, ta fuskar karfafa bada kariya da amfani da kayayyakin al’adu da kare muhalli da kuma kula da kogin Weihe.
A birnin Tianshui kuwa, Xi Jinping ya yi rangadi a gidan ibada na Fuxi da sansanin noman tuffa nau’in Huaniu na Nanshan dake yankin Maiji da kuma jerin kogo na Maijishan, domin fahimtar yadda ake daukaka karewa da gadon al’adu da kuma raya masana’antar kayan marmari ta zamani. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp