Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da yammacin jiya, inda ya ziyarci lumbunan samar da furanni masu aiki da sabbin fasahohi na zamani da tsohon garin Lijiang, don fahimtar yadda ake raya aikin gona na musamman mai la’akari da yanayin wurin, da yadda ake gaggauta karewa da amfani da kayayyakin al’adu na tarihi da aiwatar da ra’ayin dunkulewar al’umomin Sinawa.
Lambun renon furanni mai aiki da fasahar zamani na Lijiang na da fadin hekta 73.3, wanda ya hada aikin shuka da sufurin furanni da yawon bude ido tare, kuma ya habaka aikinsa zuwa harhada man furanni da samar da busassun furanni da sarrafa abinci mai hade da furanni da sauransu. A kan yi jigilar kayayyakin da ya kan samar ba kadai zuwa manyan birane kamar Beijing da Shanghai da Guangzhou da sauransu ba, har da kai su kasashen waje kamar Japan da Vietnam da Rasha da sauransu, matakin da ya samar da karin guraben aikin yi kimanin 300 a kauyukan dake kewayensa.
Yayin ziyararsa, Xi Jinping ya ce, “ku gudanar da wannan aiki da kyau, wanda ya dace da alkiblar da ake bi na zamanatar da aikin gona. Ina fatan rayuwarku za ta yi kyau tamkar kyawawan furanni.”
Garin gargajiya na Lijiang na da tarihi fiye da shekaru 800. Shugaba Xi ya ce, al’adu da shimfidar wurin da hikimomin al’ummar wannan wuri na jawo hankalin mutane sosai, kuma haduwar al’adu da sha’anin yawon bude ido na ciyar da tattalin arzikin wuri gaba. Ya kara da cewa, ya kamata a raya wannan sha’ani bisa hanya mai kyau da dorewa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp