Da maraicen yau Laraba 10 ga watan nan ne, a babban dakin taron al’umma dake Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Guinea Bissau, Umaro Mokhtar Sissoco Embaló, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar, inda shugabannin biyu suka amince da daga matsayin dangantakarsu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
A yayin shawarwarin, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin da Afirka dukkansu suna da wayewar kai mai burgewa, kuma dukkansu na dakon tarihin mulkin mallaka da mamaya da aka musu, kuma dukkansu na mutunta tare da tabbatar da ‘yancin kai da ‘yancin kasa. Kasar Sin da kasashen Afirka na taimakawa juna cikin gaskiya, kuma sun zama abin koyi na hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa. Za a gudanar da sabon taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a Beijing a wannan kaka. Kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da Guinea Bissau da sauran kasashen Afirka, domin tattaunawa kan tsare-tsaren hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a wannan sabon zamani, da kare moriyar kasashe masu tasowa, da daidaito da adalci tsakanin kasa da kasa, da yin hadin gwiwa don gina wata babbar al’umma mai makomar bai daya ga Sin da Afirka, da sa kaimi ga gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama.
- Fakewa Da Batun Kasar Sin Ba Zai Taimaka Wa NATO Cimma Burinta Da Ya Shafi Yankin Asiya Da Tekun Pasifik Ba
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
A nasa bangare, Embaló ya ce, kasar Sin ba ta taba yin mulkin mallaka ba, ba ta taba tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ba, ba ta taba yin katsalandan ga sauran kasashe ba, kuma tana girmama kananan kasashe da daidaito da mutuntawa. Kasar Sin ta kasance tana bin kalamanta da ayyuka. Abin da kasar Sin ta kawo wa kasashen Afirka shi ne makarantu, asibitoci, hanyoyi da sauran ayyukan hadin gwiwa da ke amfanar jama’ar Afirka. Kasar Guinea-Bissau ta yaba da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa, da kyakkyawar gudummawar da take bayarwa wajen taimakawa ci gaban nahiyar Afirka, kuma tana goyon bayan kasar Sin sosai wajen karbar bakuncin sabon taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka.
Bayan tattaunawar, shugabannin kasashen biyu, tare suka rattaba hannu kan wasu takardu kan aiwatar da shirin raya kasa da kasa, da raya tattalin arziki, da binciken kwastam, da nazarin kasa da ma’adinai. (Yahaya)