Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa kasar Uzbekistan a jiya Laraba, domin ziyarar aiki tare da halartar taro karo na 22 na shugabannin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO) da za a yi a birnin Samarkand na kasar.Â
Shugaban Uzbekistan, Shavkat Mirziyoyev da sauran jami’an gwamnati da suka hada da firaminista Abdulla Aripov da ministan harkokin waje, Abdulaziz Kamilov ne suka tarbi shugaba Xi bayan.
Cikin wata sanarwa, shugaba Xi ya bayyana abotar dake tsakanin Sin da Uzbekistan a matsayin wanda ya shafe tsawon shekaru 2,000 kuma har yanzu yake cike da kuzari.
Ya ce muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu ta kai ga gaggauta samar da ci gaba.
Yana mai cewa zai yi tattaunawa mai zurfi da shugaba Mirziyoyev game da yadda za su zurfafa hadin gwiwar kasashen biyu.
Bugu da kari, shugaban na Sin ya ce yana sa ran halartar taron SCO na Samarkand, da kuma aiki da dukkan bangarori domin raya ruhin kungiyar, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna, da ingantawa da raya kungiyar. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)