Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa tattaunawar da Sin da Amurka suka yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump gobe Alhamis a Busan na Koriya ta kudu, inda za su yi musanyar ra’ayi kan batutuwan da suke jawo hankalin bangarorin biyu. (Amina Xu)














