Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar da cewa, tsakanin ranakun 27 zuwa 28 ga watan Yulin, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude gasar wasannin motsa jiki na daliban jami’o’in kasa da kasa ta lokacin zafi karo na 31 da za a yi a birnin Chengdu na kasar Sin, inda zai gana da shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin, a wajen liyafar maraba da zuwansu.
Kuma, shugabannin da za su halarci bikin bude gasar da kuma kai ziyarar aiki a kasar Sin, sun hada da shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo, da shugaban kasar Mauritania ta Musulunci Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani, da shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye, da shugaban kasar Guyana Mohamed Irfaan Ali, da firaministan kasar Georgia Irakli Garibashvili, da kuma firaministan kasar Fiji Sitiveni Rabuka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)