Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Afirka ta Kudu, inda zai halarci taron ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 15 da za a gudanar a birnin Johannesburg na kasar tsakanin ranakun 21 zuwa 24 ga watan Agusta, bisa gayyatar da shugaban kasar Matamela Cyril Ramaphosa ya yi masa.
Kuma, a yayin ziyararsa a kasar Afirka ta Kudu, shugaba Xi Jinping da shugaba Matamela Ramaphosa za su jagoranci taron tattaunawa tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp