Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da wakilan da suka halarci aikin binciken sararin samaniya na kumbon Chang’e-6 da safiyar yau Litinin a birnin Beijing, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.
Xi ya bayyana cewa, kumbon Chang’e-6 ya gama aikin kwaso samfura daga bayan duniyar wata karo na farko a tarihin bil’adama, yayin aiwatar da wasu fasahohi masu muhimmanci, wanda hakan ya zama sakamako da Sin ta samu a fannin gina kasa mai karfin binciken sararin samaniya da kimiyya da fasaha.
Xi ya kara da cewa, sararin samaniya na waje, fili ne na bai daya ga daukacin dan Adam, kuma binciken sararin samaniya aiki ne na bai daya ga dukkan dan Adam. Don haka ya kamata a ci gaba da bude zuciya, a zurfafa gudanar da nau’o’in hadin gwiwar kasashen duniya a fannin binciken sararin samaniya, kana a raba sakamakon ci gaba tare da sauran kasashe, da kyautata tsarin tafiyar da harkokin sararin samaniya, domin a yi amfani da sakamakon kimiyya da fasahar binciken sararin samaniya wajen amfanar dukkanin ɗan Adam. (Safiyah Ma)