A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Iran Ebrahim Raisi, wanda ya fara ziyarar aiki ta yini 3 a kasar Sin.
Yayin zantawar su, shugaba Xi ya ce duk yadda yanayin harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi ya sauya, Sin za ta tabbatar da gina kawancen hadin gwiwa tare Iran. Kaza lika Sin za ta goyi bayan Iran din wajen kare ikon mulkin kai, da ‘yancin jagoranci, da tsaron yankuna da martabar kasar.
Har ila yau, Sin ba ta taba amincewa da mayar da wasu sassa saniyar ware ba, ko cin zali, ko tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran, ko duk wasu matakai da za su haifar da koma-bayan tsaro da daidaito a kasar. Bugu da kari, Sin a shirye take da ta ci gaba da tabbatar da goyon bayan juna, kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar sassan biyu.
Shugaba Ebrahim Raisi, ya fara ziyarar aiki ta yini 3 a Sin tun daga Talatar nan, kuma wannan ce ziyarar sa ta farko a wata kasar waje, cikin shekarar nan ta 2023, kana karon farko da yake ziyarar aiki a Sin, tun kama aikin sa a matsayin shugaban Iran a watan Agustan shekarar 2021.
Kafin barin sa gida, Raisi ya wallafa wata makala a jaridar “People’s Daily” ta Sin, wadda a ciki ya jaddada cewa, har kullum Iran na aiwatar da manufofin karfafa alaka da kasar Sin, kuma ba za ta bari, yanayin da ake ciki a matakin kasa da kasa, da na yankin su ya shafi wannan kyakkyawar dangantaka ba. (Saminu Alhassan)