A yau Lahadi 5 ga wannan wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon taya murna ga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na shida da aka kaddamar a birnin Shanghai na kasar Sin.
A cikin sakonsa, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, an yi nasarar shirya bikin sau biyar tun daga shekarar 2018, lamarin da ya taimaka matuka wajen kafa sabon tsarin ci gaban duniya da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
- Dabarun Samun Kudi Ga Matan Aure Ta Hanyar Fasahar Sadarwa – Hajiya Hafsat
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Iyakar Kokarin Saukaka Rikicin Gaza
Haka kuma Xi ya jaddada cewa, har yanzu ba a kai ga farfado da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata ba, don haka akwai bukatar kasashen duniya daban daban su hada kai tare da yin hadin gwiwa a tsakaninsu domin samun ci gaba tare. Kuma a ko da yaushe kasar Sin tana samar da damammaki ga sauran kasashen duniya, ta hanyar bude kofarta ga ketare.
Rahotanni sun nuna cewa, a yau ne aka kaddamar da bikin CIIE karo na shida, firayin ministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya domin samun ci gaba tare. (Mai fassara: Jamila)